News

DUBU TA CIKA: Asirin Wani Mutun Ya Tonu Bayan Ya Daɗe Yana Kaiwa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A Ƙaramar Hukumar Jibia Dake Jihar Katsina

DUBU TA CIKA: Asirin Wani Mutun Ya Tonu Bayan Ya Daɗe Yana Kaiwa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A Ƙaramar Hukumar Jibia Dake Jihar Katsina

DAGA Comr Nura Siniya

Kamar yadda kuke gani Shugaban ƙaramar hukumar Jibia ne Hon. Bashir Sabi’u Maitan, ya kama wani mutum da hannun shi mai suna Aminu Gangara da ya shahara wajen bada bayanan sirri ga ƴan bindiga.

(Informer) wanda ake zargin yana da hannu dumu-dumu a ta’addancin da ake a garin Bugaje da Gangara da kuma garuruwan da suke ƙarƙashin Masarautar Ɗaɗɗara dake Jibia a jihar Katsina

A rahoton da muka samu an zargi Aminu Gangara da kaiwa ƴan bindiga bayanan sirri akan wani Attajirin yankin da barayin dajin suka ɗauka Alhaji Tasiu Waliyi da sauran wasu mutane a yankin.

Muna roƙon Allah ya ƙara tona asirin duk wani mai hannu a cikin taɓarɓarewar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa da Najeriya baki ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button