News

Fadar Sarkin Kano ta baiwa Air Peace sa’o’i 72 ya ba ta haƙuri ko ta ɗauki mataki

Fadar Sarkin Kano ta baiwa Air Peace sa’o’i 72 ya ba ta haƙuri ko ta ɗauki mataki

Fadar Sarkin Kano ta baiwa kamfanin jirgin sama na Air Peace wa’adin sa’o’i 72 da ya ba da hakuri kan rashin girmamawar da ta ce ya yi wa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Babban hadimin Sarkin, Isa Bayero, ne ya bada wa’adin lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Kano a jiya Asabar.

Isa Bayero ya bayyana cewa dole ne kamfanin jirgin ya karɓi alhakin jinkirta tashin jirgin da Sarkin ya hawo da ga Banjul, wanda ya kai ga rashin girmamawar da basu yi wa sarkin ba.

“Ina ba da wa’adin sa’o’i 72 ga Air Peace da su baiwa sarki haƙuri. Na farko dai sai sun bashi hukuri a manyan jaridun ƙasar nan, na biyu kuma su bashi haƙuri baki da baki. Idan kuma ba haka ba, za mu bi kadin abin da suka yi”.

Ya kuma yi watsi da iƙirarin da kamfanin jirgin ya yi na bai wa sarkin damar sauya masa jirgi zuwa wanda zai je Abuja.

“Ni da kaina na nemi kamfanin Air Peace na ba wa sarkin damar shiga jirgin su zuwa Abuja; Daga nan za mu taho zuwa Kano amma su ka ce shi ma jirgin da zai tafi abujan ya cika,” in ji Isa Bayero, wanda a ka fi sani da Isa Pilot.

Ya kuma ƙara da cewa, jinkirin da su ka samu daga Banjul, shi ne ya yi sanadin isowarsu Legas a makare, kuma kamfanin na Air Peace shi ya ke da alhakin kula da su, amma bai yi hakan ba kuma ma’aikatan sa su ka bar su hakan nan.

“Abin da Kamfanin na Air Peace suka yi abu ne na rashin kwarewa kuma za mu yi iya kacin ƙoƙarinmu don daukar matakan da su ka dace akan rashin ɗa’ar da a ka yi wa sarkin mu.” Inji Isa Pilot

“Wannan cin mutuncin ba Sarki kadai a ka yiwa ba, har da mutanen Kano baki ɗaya kuma ba za mu zura Ido hakan ta ci gaba da faruwa ba,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button