News

Gwamna Abba Ya Yabawa matashin da ya Maidowa da Gwamnati Albashin mahaifinsa da aka cigaba da biya Al’halin Kuma ya rasu.

Gwamna Abba Ya Yabawa matashin da ya Maidowa da Gwamnati Albashin mahaifinsa da aka cigaba da biya Al’halin Kuma ya rasu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, a yau ya karbi bakuncin Yusuf Sulaiman Sumaila, matashin da ya mayar wa gwamnatin jihar albashin mahaifinsa da aka cigaba da biya bayan mahaifin nasa kuma ya rasu.

Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da biyan albashin mahaifinsa da ya rasu a cikin asusunsa na banki bayan rasuwarsa a watan Oktoban 2022 har zuwa watan Agustan 2023, inda ya bukaci a dakatar da biyan albashin.

Inda gwamnan ya gamsu, Yusuf ya kuma bukaci a mayar wa gwamnati kudaden da suka kai 328,115.75, wanda kuma gwamnan da kan sa ya gayyace shi ofishin sa don yi masa godiya.

Da yake nasa jawabin, gwamnan ya yabawa Yusuf bisa wannan gagarumin karimcin da ya nuna, inda ya bukaci sauran matasa su yi koyi da shi, su kuma kiyaye darajar gaskiya.

Abdullahi I. Ibrahim
SSA, Digital Media

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button