News

Jarumi Ali Nuhu Yabi Sahun Masu Zanga-Zangar Lumana Ta Rashin Tsaro A Yankin Arewa

Jarumi Ali Nuhu Yabi Sahun Masu Zanga-Zangar Lumana Ta Rashin Tsaro A Yankin Arewa

Ya kamata masu alhakin tsaro a kasar nan su agaza wajen karbo yaran makarantar FUGUS. Su ma ya’ ya ne kuma suna cikin matsanancin hali sannan iyayensu da yan’uwasu suna cikin tashin hankali

Inji ali nuhu

TSARON NIGERIA YA SHIGA WANI HALI MARAR KYAU

Wato an yiwa matakan tabbatar da tsaron Nigeria illar da za’a dauki tsawon lokaci ana shan wahala kafin lamura su daidaita

Ba zaku fahimci hakan ba sai kun kalli wannan Bidiyo har karshe kun tambayi masana tsaro sun muku sharhi akan bidiyon

Sojojin Nigeria ne suke sulhu da fulanin jeji masu garkuwa da mutane, sojojin suna rokon barayin akan su dena tare hanyar Funtua zuwa Tsafe

Hanyace wanda manyan mutane suke bi, ma’ana idan sun dena tare hanya su koma kauyuka kenan su cigaba da cutar da talakawa masu karamin karfi

Jama’a ku duba ku gani fa, Wai Sojan Nigeria ne yake sulhu da ‘yan bindiga, wannan babbar illa ne wa tsaron Kasa, kuma alkalami ne da yake nuna mana cewa tsaron Nigeria tayi muguwar lalacewa

Ba aikin Soja bane shiga sulhu da bandits, wannan zubar da kimar Soji ne kuma zubar da kimar Kasa

Shin menene ma ya kawo Soja cikin internal security imba lalacewa ba, ba aikinsu bane, ya zama wajibi masu iko da Nigeria su yiwa hukumomin tsaron Nigeria garambawul tare da janye Sojoji daga shiga cikin internal security domin a dawo da kwarjini da martabansu

Muna fatan Allah Ya gyara mana tsaron Nigeria Ya mana maganin maciya amana

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button