News

Harin Yan Bindiga Zamfara. Bayan An Binne Mutum 90 Ana Neman Wasu

Harin da yan bindiga suka kai a zamfara, adadin mutanen da suka rasa rayukan su na kara yawa yayinda wasu rahotanni suka tabbat da cewa akalla an bizne mutum 90.

Wadansu da Abin ya shafi sun bada bayani game da halin da ake ciki game da lamarin.

Sunusi na’ibi shine babban limamin kauyen kuma shine ya jagoranci yiwa mamatan Sallah.

Mazauna magami sun tabbatar da cewa sun bizne mutum 60, Bayan nan kuma sun gano wasu 53.

Wata majiya ta bayyana cewa a wannan mummunan harin Anfi yiwa karamar hukumar gusau illa domin kisa kawai sukazo yi ba sata ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button