Maigirma Sheikh Abduljabbar Kabara yakai ziyarar ta’aziya gidan Barrister Abdullahi Ado Bayero (Alajin Mama) sakamon rasuwar Mahaifiyarsa Hajiya Maryam Ado Bayero Mai Babban Dakin Kasar Kano da kuma Kasar Bichi wacce Allah yayiwa rasuwa a yau Assabar a kasar Masar.

A ziyarar tasa Sheikh Abduljabbar Kabara yayi Addu’a kuma yaroki Allah yajikan Hajiya Maryam Ado Bayaro Allah yagafarta mata yayi mata rahama Allah ya gatta kwanciya Allah yasa tana aljanna madaaukakiya iyalanta kuma Allah yabasu hakurin juere rashinta Amin.

Daga…
Comr. Jamilu Wahada
Ashabulkahfi Social Media Team
April 24th, 2021.

Click Here To Drop Your Comment