NewsPolitics

Hukumar ICPC Na Neman Sirikin Shugaba Buhari Ruwa A Jallo. Kan Almundahanar $65m

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta bayyana Gimba Kumo, Wanda daya ne daga cikin sirikan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda hukumar take nema ruwa a jallo a bisa zargin almundahanar kudi dalar Amurka har $65m na daga cikin kudaden samar da gidaje ga ma’aikata. Kamar yadda shafin Jaridae BBC HAUSA Suka Wallafa A Shafinsu Na Facebook.

Idan ba’a manta ba A 2016 ne Mr Kumo, tsohon daraktan gudanarwa na bankin Federal Mortgage ya auri yar shugaban kasa muhammadu Buhari a Daura da ke jihar Katsina.

Cikin wani jadawali da hukumar ta fitar ta ICPC ta bayyana Mr Kumo tare da Tarry Rufus da Bola Ogunsola a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo saboda zargin tafka almundahana.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ICPC, Azuka Ogugua, Hukimar ta ICPC ta bukaci jama’a su gabatar mata da duk wasu bayanai da suka sani wanda kuma za su taimaka hukumar wajen gano inda wadannan mutanen suke.

“Duk wanda yake da wani bayani kan inda mutanen suke yana iya ba da rahoto ga hedikwatar ICPC da ke Abuja ko ofisoshinta na jihohi ko ma ofishin yan sanda da ke kusa,” kamar yadda aka rubuta a takardar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button