News

Yanzu-Yanzu Yan Bindiga Sun Shiga Kotu Tare Da Yin Garkuwa Da Alkalin Kotun A Jihar Katsina

Wasu Rahotanni da Muke Samu Yanzu Yanzu Na Cewa Wasu ‘yan bindiga sun kutsa kai zauren Wata kotu Dake kauyen Bauren Zakat A karamar hukumar Safanar jahar Katsina

Tare Da yin awon gaba da alkalin mai suna Alhaji Husaini Samaila a ranar Talata da misalin karfe uku na yammaci

Rahotannin sun kara da cewa, gwamnati ce ta mayar da kotun izuwa karamar hukumar Safana saboda rashin tsaro

Kamar yadda shedun gani da ido suka sanar da Daily Trust cewa,

Yan bjndigar sun balle kofar kotun tare da chusa kai cikin harabar kotun da misalin karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma suka yi awon gaba da alkalin mai suna Alhaji Husaini Sama’ila.

Har yanzu dai an kasa gano wanne dalilin ne ya kai alkalin kotu. duk da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a a Najeriya (JUSUN) ke ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button