News

Zamfara: Dole Ne Manoma Su Fara Aiki A Gonakin Mu Kafin Suyi A Nasu Inji Shugaban Yan Bindiga Dogo Gide

Shugabannin Yan Bindigar Jihar Zamfara Sun Kafa Sharadi Wa Manoma, Dole Ne Manoma Su Fara Noma Gonakin Su Kafin Daga Bisani Su Noma Tasu A Cewar Shugabannin Yan Bindigar Dogo Gide.

Wani Mazaunin Jihar Zamfara Ya Tabbatar Da Cewa Sun Tafi Gonar Black Da Ta Gide Su Fara Sharar Gona Kafin Daga Bisani Su Dawo Tasu.

Shugabannin Yan Bindigar Sun Tabbatarwa Da Manoman Cewa Zasu Kare Su Sannan Su Kyale Su Amma Sai Sunyi Aiki A Gonakin Su Tukunna Kafin Suyi A Nasu.

Kamar Yadda Jaridar Daily trust Ta Rawaito, tuni manoman Suka fara aikin gonar black baki dakuma dogo gide domin kaucewa abinda ka iya zuwa ya dawo don gudun tsira da rai.

Kamar Yadda Wani mazaunin garin Dansadau mai suna Bilyaminu Dansadau ya Shaidawa Jaridar Daily Trust cewa, wasu daga cikin manoman kauyukan dake kusa da Babbar Doka dake kusa da Dansadau a karamar hukumar Maru, Tuni suka fara zuwa gonar Dogo Gide domin gyaranta kafin daga bisani su wuce zuwa gonar black.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button