News

Yanzu-Yanzu Allah Yayiwa Babban Hafsan Sojojin Nigeria Attahiru Ibrahim Rasuwa

rahotannin Da Muke Samu Yanzu Yanzu Sun Rawaito Cewa Allah Yayiwa Babban hafsan sojan Najeriya Ibrahim Attahiru Rasuwa A Bisa Hatsarin Jirgin Sama Da Ya Rutsa Dashi a Kaduna,

Kamar Yadda Jaridar Daily Nigerian Ta Rawaito Cewa.

bayanan da ke zuwa ga jaridar DAILY NIGERIAN sun Kara Da cewa babu wani wanda ya tsira daga hatsarin.

Bayanai sun Kara Da cewa jirgin ya yi hadari fadi a filin jirgin saman Kaduna da misalin karfe 6 na yamma yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya.

An dai nada Mista Attahiru a matsayin babban hafsan hafsoshin soja a ranar 26 ga watan Janairu, wanda ya gaji Tukur Buratai. Kuma Ya na da shekaru 54. Mista Attahiru Ya Rasu tare da wasu shugabannin sojoji da ke jirgi daya, in ji majiyoyin

Tuni Dai aka Sanar Da fadar shugaban kasa Game Da Batun

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button