News

Igbo Ya Samu Galaba A Kotu Bayan Dirkawa Bahaushiya Ciki A Kebbi

Igbo Ya Samu Galaba A Kotu Bayan Dirkawa Bahaushiya Ciki A Kebbi

Daga : Engr. Adamu Attahiru

Wani Igbo ya samu galaba a kotu ta hanyar beli bayan da ya dirkawa wata Bahaushiya ciki a Birnin-Kebbi.

Wannan lamari yana zuwa ne a wani yanayi mai kama da na Bahaushen da ya auri Igbo a Jihar Bayelsa wato Yunusa Yellow, wanda yanzu haka yake fuskantar zaman kaso.

Wasu masu fafatukar kare hakkin Dan’adam sun lashi takobin bibiyar wannan Shari’a wadda suke ganin wata kabila tana son yin amfani da karfi domin ganin sun lalata shari’ar saboda ta shafi dan yankin su.

Yanzu haka dai Onyebuchi Okafor tuni ya fito yana yawonsa ko’ina a cikin Birnin-Kebbi yana kuma neman hakkin a ba shi ‘yarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button