News

IKON ALLAH: An Samu Wata Zuri’ar Da Da Zarar Sun Kai Shekara 18 Sai Su Kamu Da Cutar Mutuwar Jiki (Faralayiz) A Jihar Nasarawa

IKON ALLAH: An Samu Wata Zuri’ar Da Da Zarar Sun Kai Shekara 18 Sai Su Kamu Da Cutar Mutuwar Jiki (Faralayiz) A Jihar Nasarawa

Daga Aliyu Ahmad

Babu shakka Allah shine mai yin yadda Ya so kuma a duk lokacin da Ya so.

Wata zuri’a a garin Gitata dake karamar Hukumar Karu ta jihar Nasarawa, sun tsinci kan su cikin wata jarabta ta Allah wadda da zarar su kai shekaru 18 a duniya za su kamu da ciwon mutuwar sassan jiki (faralayiz). Inda ba za su kara iya wani aiki da gabobinsu ba, komai saidai a yi musu.

Zuri’ar wanda su bakwai ne suke a raye, yanzu haka kusan shida daga cikin su ba sa moruwa, inda ‘yar autar su daya tilo da take da lafiya ita ke dawainiya da su.

Kasancewar zuri’ar suna bukatar taimak√≤ ga ahi kuma sun kasance marayu (ba su da uwa da uba), wanda hakan ya sa Gidauniyar Al-ihsan Foundation ta kai musu tallafin kayan abinci karkashin jagorancin Shugabanta, Ibrahim Bashir Ahmad (Ya Malam).

Gidauniyar ta Al-Hisan ta kuma baiwa wasu mabukata dake makwabta da marasa lafiyan da kayan abinci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button