Politics

Ina Mai Yabawa Hukumar INEC Ta Kasa Bisa Yadda Ta Soke Nasarar Zaben Gwamnan Adamawa Da Aka Ce Binani Ta Yi, Cewar Gwamna Fintiri

Ina Mai Yabawa Hukumar INEC Ta Kasa Bisa Yadda Ta Soke Nasarar Zaben Gwamnan Adamawa Da Aka Ce Binani Ta Yi, Cewar Gwamna Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce ya ji takaicin yadda wani jami’in INEC ya bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar gabanin kammala tattara alƙaluman zaɓen.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya shirya taron manema labarai, biyo bayan sanarwar da INEC ta fitar ta dakatar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Wannan na zuwa ne bayan halin da jihar ta tsinci kanta a ciki na ruɗani, bayan da ɗaya daga cikin jami’an INEC ya sanar da cewa ‘yar takarar gwamna ta APC Aisha Dahiru Binani ce ta lashe zaɓen gwamnan.

Tuni dai hankula suka koma kan jihar domin sanin wanda zai lashe zaɓen tsakanin ‘yan takarar biyu.

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta ce ta ayyana dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa

Cikin wata sanarwa da babban jami’inta kan harkar yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Barista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa ya bi na sanar da wanda ya lashe zaɓe haramtacce ne, ta ce don haka ba za a yi amfani da shi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button