News

INNALILLAHI: Ku Kalli Yadda ’Yan Bindiga-daɗi Suka Sace ’Yan Yawon Sallah A Jahar Katsina

Ku Kalli Yadda ’Yan Bindiga-daɗi Suka Sace ’Yan Yawon Sallah A Jahar Katsina

Daga Zaharaddeen Gandu

’Yan bindiga-daɗi sun kai hari kan wasu ’yan yawon Sallah a katsina, tare da k@she ɗaya daga cikinsu, da kuma yin garkuwa da wasu biyu a jihar ta Katsina.

’Yan bindigar sun kai wa ’yan yawon Sallan da ke hanyarsu ta dawowa daga Katsina hari ne a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

’Yan yawon sallan sun yi mugun gamon ne a wani shingen tare ababen hawa da bata-garin suka kafa a kan hanyar.

Matashin da ’yan bindigar suka kashe, Anas Adamu, ɗalibin ajin ƙarshe ne a Kwalejin Ilimi da ke Katsina.

Wani abokin mamacin, Muhammad Aliyu, ya bayyana mana cewa, “bayan ’yan bindigar sun kafa shingen a cikin dare ne, yayin da motocin matasan suka kutsa cikinsu a bisa kuskure”.

“Bayan bukukuwan Sallah sun baro cikin birnin Katsina da misalin 8:30 na dare zuwa ƙaramar hukumar Jibiya”.

“A hanya, sai motar da ke gaba ta ga shingen a kurkusa ta fada ciki, amma direban ya yi sa’a, ya sake dawo da motar kan titi, suka tsere”.

“Mota ta biyu da ta uku kuma ’yan bindigar sun riga sun far musu, suka harbi ɗayan direban a kafa suka yi ƙoƙarin sace sauran mutum biyu da ke cikin motar”.

“Shi kuma mamacin ya yi ƙokmƙarin tserewa, amma suka kama shi suka riƙa saran shi, suka karya mishi hannu da ƙafa, sannan suka yayyafa mishi wuta, a haka ya rasu.” inji abokin mamacin.

Saide a yayin haɗa wannan rahoton, mun tuntuɓi kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma ya ce ba shi da labari a kan wannan lamarin.

Sai dai ya ce zai tuntuɓi DPO na yankin ƙaramar hukumar Jibiya domin ƙara samun bayanai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button