News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 50 A Jihar Jigawa

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 50 A Jihar Jigawa

Wasu alkaluman hukumar agaji ta Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 50 sakamakon ambaliyar ruwan da yankin arewacin kasar ya fuskanta biyo bayan kakkarfan ruwan saman da ake ci gaba da samu tun daga watan Yuni zuwa yanzu.

Hukumar agajin gaggawa ta jihar jigawa SEMA, ta ce duk da kasancewar jihar a sahun wadanda ke fuskantar ibtila’in ambaliyar kowacce shekara, a wannan karon lamarin ya tsananta fiye yadda masana suka yi hasashe.

Shugaban hukumar ta SEMA, Yusuf Sani ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa ambaliyar ta faru a kananan hukumomin jihar 27 kuma zuwa yanzu akwai alkaluman mutum 50 da aka tabbatar sun mutu sanadiyyar ambaliyar.

Yusuf Sani ya ce kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata, su suka kasance mafiya tayar da hankali ta yadda aka ga zubar ruwan sama babu kakkautawa a cikinsu.

Shugaban hukumar ta SEMA ya ce zuwa yanzu sun kirge dubunnan mutane wadanda ibtila’in ya shafa kuma sun cikin halin bukatar agajin gaggawa.

Karamar hukumar Kafin Hausa na matsayin yankin da matsalar ta ambaliyar ruwa ta fi yiwa barna inda ta kashe mutane 10 sai wasu 68 da ke kwance a asibitoci kana ta raba wasu mutane dubu 1 da 436 da muhallansu galibi daga kauyen Balangu da ambaliyar ta rushe gidaje 237.

Zuwa yanzu jihar ta jigawa ta samar da matsugunan wucin gadi 11 don killace wadanda ambaliyar ta shafa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button