News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un: Bidiyo Yadda Jami’an Tsaro Suka Rushe Kasuwar Dare Dake Asokoro A Abuja, Tare Da Kashe Mutane Ta Hanyar Harbi

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un: Yadda Jami’an Tsaro Suka Rushe Kasuwar Dare Dake Asokoro A Abuja, Tare Da Kashe Mutane Ta Hanyar Harbi

Rahotannin Da Muke Samu Yanzu Yanzu Daga Nura Ahmad Sokoto Wanda Aka Wallafa A Shafin Jaridar Rariya Facebook Na Cewa.

A yau Laraba da misalin karfe 3:30, jami’an tsaro sun kai farmaki a Kasuwar Dare da ke unguwar Asokoro Village a cikin birnin tarayya Abuja.

Inda su ka rushe wajen da matasa ke gudanar kasuwancin su na miliyoyin kudi ba tare da sun umurce mazauna gurin da su kwashe kayan su na miliyoyin kudi ba.

A cikin wannan aika-aika, jami’an tsaron sun kashe matasa 4 tare da raunata wasu 8 ta hanyar harbin mai kan uwa da wabi.

Wannan matashi mai suna Ibrahim dan asalin jihar Sokoto yana daga cikin matasan da aka kashe a wannan lamari na rashin imani.

Akan haka muna neman shugabannin mu musamman na jihar Sokoto da su bi mana hakkin wannan cuta da aka mana.

Daga Nura Ahmad Sokoto

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button