News

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Yadda Wasu Mutane Suka Nutse A Cikin Ruwa Yayin Da Suke Tserewa Harin ‘Yan Bindiga

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Yadda Wasu Mutane Suka Nutse A Cikin Ruwa Yayin Da Suke Tserewa Harin ‘Yan Bindiga

Wasu mata da kananan yara da dama ne suka nutse a ruwa a lokacin da suke kokarin tserewa wani harin yan bindiga dauke da makamai a yankin arewacin Najeriya mai fama da rikici, kamar yadda mazauna yankin da wani jami’in gwamnati suka bayyana a jiya Alhamis.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu ne a lokacin da kwale-kwalen su ya kife a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai musu hari na tsawon sa’o’i a daren Laraba a yankin Birnin Waje da ke jihar Zamfara, in ji wani mazaunin garin Ibrahim Zauma.

“Al’amarin ya yi muni saboda yawancin mutanen sun gudu daga gidajensu. Gawarwakin da aka gano kawo yanzu dai sun kai 13,” in ji Zauma.

Ba a dai bayyana ko nawa ne suka nutse ba, amma da dama da suka tsere daga gidajensu ba su koma yankin ba, lamarin da mazauna yankin suka ce ya kasance cikin rudani fiye da sa’o’i 24 bayan tashin hankalin.

Mai magana da yawun gwamnatin Zamfara, Ibrahim Bello, ya tabbatar da faruwar hatsarin, yana mai cewa “ba a san adadinsu ba, yawancin mata da kananan yara ne suka nutse a ruwa” yayin da suke neman tserewa a cikin kwale-kwale guda biyu.

Sai dai bai bayyana ko an kama yan bindigan ba.

Harin dai na daya daga cikin hare-hare na baya-bayan nan a jerin tashe-tashen hankula da kungiyoyi masu dauke da makamai suka kai wa al’ummomin yankunan arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar Najeriya.

Hukumomin kasar sun dade suna dora alhakin kai hare-haren kan gungun mafi yawan matasa makiyaya ‘yan kabilar Fulani da rikicin Najeriya ya rutsa da su tsakanin al’umma da makiyaya kan karancin ruwa da filaye.

Rikicin da ya janyo asarar rayuka tsakanin al’ummar yankin da makiyaya ya  sha kan matakan da gwamnati ta dauka na kwantar da tarzoma, ko da yake a baya-bayan nan jami’an tsaro sun sanar da kama wasu da kwace makamai.

‘Yan bindigan a yawancin al’ummomin da abin ya shafa sukan fi karfin Jami’an tsaron Najeriya yayin da hukumomi kuma ke ci gaba da yakar tada kayar bayan da ‘yan tawaye masu kaifin kishin Islama suka kaddamar a yankin arewa maso gabas na tsawon shekaru goma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button