News

Innalillahi.. Yadda Wata Mata Ta Sa Aka Kashe Mijinta Saboda Zai Kara Aure A Jihar Kebbi

Innalillahi.. Yadda Wata Mata Ta Sa Aka Kashe Mijinta Saboda Zai Kara Aure A Jihar Kebbi

Wannan bawan Allah Lauya ne, sunansa Barr Attahiru Ibrahim Zagga daga jihar Kebbi, yana da mata amma sun rabu sakamakon bakin kishi na jahilci da ta tayar saboda yana shirin kara aure.

Yau saura kwana 7 a daura masa aure da sabuwar amaryansa da zai aura a Maiduguri, to sai shekaran jiya matarsa da suka rabu ta nemo ‘yan ta’adda suka tafi gidansa suka rutsa shi, suka dinga caccaka masa wuka har sai da hanjin cikinsa ya fito.

‘Yan ta’addan sun samu nasaran tserewa, amma ita matar an kamata kafin ta tsere, yanzu haka tana State CID na jihar Kebbi

Zaku ga gashi har da invitation card dinsa zai kara aure, tsohuwar matarsa ta kashe shi saboda laifinsa kawai zai kara aure bata so.

Muna fatan Allah Ya jikan Barr Attahiru, Allah Ya tona asirin duk wanda yake da hannu a kashe shi.

Daga Datti Assalafiy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button