News

Jaruma Rahama Sadau Ta Aika Sako Tare da Yin Gargadi ga Gwamnatin Buhari Akan kashe ‘Yan Arewa da Ake

Jaruma Rahama Sadau Ta Aika Sako Tare da Yin Gargadi ga Gwamnatin Buhari Akan kashe ‘Yan Arewa da Ake

Ficacciyar Jarumar Masana’anyar Kannywood Rahama Sadau tayi gargadi akan Gwamnatin shugaba Muhammad Buhari kan cewa, su shiga taitayin su kada al’ummar Nageriya su fusata.

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana hakan ne wata wallafa da tayi a shafin ta na sada zumunta Instagram inda take cewa, rayukan al’ummar Nageriya ba’a bakin komai yake ba domin a yanzu ‘Yan Bindiga sun amamaye ko ina a yankin Arewa suna kashe Mutane yadda sukaga dama kuma babu abin da aka yi.

A sakon da Jaruma Rahama Sadau ta wallafa a shafin nata na sada zumunta ta fadi cewa, tura takai bango a yanzu kan abubuwan da suke faruwa a Arewacin Nageriya.

Ga cikekkiyar wallafar da Jaruma Rahama Sadau tayi a shafin nata na Instagram.

Irin hotunan da muke gani ana saka wa a shafukan yanar gizo hutunan ne masu tada hankali matuka, abin tambaya menene talakawan najeriya suka yi da aka bari wadannan mutane na gallaza musu azaba.

Wai shin laifin mu shine kawai don mun Zabe su Ina nufin dukkan su da ke kan mulki a kasar nan wai yaushe za’a sauraremu a kawo mana dauki, a maida hankali wajen kawo karshen kisan gillar da ake yi wa mutane musamman ‘yan Arewa a yanzu idan kuka ji sun garzayo sun waiwaye mu to shekarar zabe ya kunnu kai ne.

Wannan rashin tsaro yana gidan kowa a yankin Arewa adai yi hattara kada allura ta hako garma, Talaka a yau zama a cikin gidansa ma tsoro yake bashi.

Idan kowa ya mutu Sai muga wanda zai zabe su zubar da jinin ya isa haka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button