News

KISAN DEBORAH: Haramun Ne Daukar Doka A Hannu, Duk Da Idan An Kai Wurin Hukuma Ba Sa Yin Abinda Ya Dace, Cewar heikh Dr. Sani Sharif Umar Bichi

KISAN DEBORAH: Haramun Ne Daukar Doka A Hannu, Duk Da Idan An Kai Wurin Hukuma Ba Sa Yin Abinda Ya Dace, Cewar heikh Dr. Sani Sharif Umar Bichi

Sheikh Dr. Sani Sharif Umar Bichi shugaban kungiyar Izala mai hesikwata a Jos rashen jahar Kano ya yi jan kunne ga waɗanda suka kashe Deborah, ya ce ba hurumin su bane yanke hukuncin kisa akan wannan daliba da ta zagi Annabi SAW.

Malam ya ce “yanzu idan aka ce wadanda suka kasheta su bada sheda kota muryar ta ba za su gane ba sabida ba ta raye, amma da an kaita gurin hukuma a yi bincike a hukumance a yanke mata hukunci daidai da abinda ta yi”.

Malam ya kara da cewa “duk da idan aka kai gurin hukuma ba sa yin abin da ya dace, ko da wani abu na laifi ya faru, babu wani wanda yake da hakkin zartar wa wani haddi ko hukunci akan tuhumar da ake masa, har sai an gabatar da shi gaban alkali, shi ne wanda zai iya tabbatar masa da wannan laifin ko ya wanke shi idan kuma hukuma ta take gaskiya ita da Allah.

“Don haka dole ne jama’a su fahimci cewa rashin bin doka ba zai taba haifar da ‘da mai ido ba.

“Yanzu wannan matashi da aka kashe mana a Sokoto duka yana daga cikin rashin bin doka kuma rashin bin doka ba zai taba zama hukuncin Allah ba kuma ba zai taba zama hanya ta nuna kauna ga Annabi Muhammad (SAW) ba”.

https://youtu.be/TwJjlH2f9gk

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button