News

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta umurci mambobinta a kasa su shirya yin zanga-zangar lumana a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta umurci mambobinta a kasa su shirya yin zanga-zangar lumana a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

CAN za ta yi wannan zanga-zangar ne domin nuna kin amincewarsu da kisar Deborah Samuel a Sokoto wacce matasa suka kan batanci ga Annabi (SAW).

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta umurci mambobinta a kasa su shirya yin zanga-zangar lumana a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022 CAN za ta yi wannan zanga-zangar ne domin nuna kin amincewarsu da kisar Deborah Samuel a Sokoto wacce matasa suka kan batanci ga Annabi (SAW) Sanarwar ta CAN ta ce za a yi zanga-zangar ne a haraban sakatariyar CAN a jihohin Najeriya ba kan tituna ba domin kada a sake rasa rayyuka

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard. Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

 

Karin Bayani 👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button