Religion

BIDIYO: Sheikh Ahmed Gumi, ya ce wadanda ba musulmi ba sun sha zagin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a lokacin da ya ke raye, amma bai taba kowa ba ko kashe masu yi masa batanci.

Fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Gumi, ya ce wadanda ba musulmi ba sun sha zagin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a lokacin da ya ke raye, amma bai taba kowa ba ko kashe masu yi masa batanci.

Malamin, kamar yadda ya furta a wani bidiyo da Ahmad Bulama ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce manzon Allah bai yi ramuwa ko kashe wadanda suke cutar da shi da zaginsa ba don kada a rika yayatawa cewa Annabi na kashe abokansa.

Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke magana kan kashe daliba kirista yar makarantar Shehu Shagari ta Ilimi a Sokoto kan zarginta da furta kalaman batanci ga Manzon Allah.

Ya bayyana cewa hanyar da ta fi dacewa musulmi su nuna kaunar su ga Annabi Muhammad (SAW) shine abi koyarwar sa sau da kafa a maimakon kashe mutane kan wasu abubuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button