News

Rashin Tsaro: Bidiyon Yadda Ta hadu da iyalin ta bayan shafe shekaru 8 a hannun yan ta’addan Boko Haram.

Rashin Tsaro: Ta hadu da iyalin ta bayan shafe shekaru 8 a hannun yan ta’addan Boko Haram.

Aliyu Samba

Wata mata mai suna Shetu Sangayama mai shekaru 30 ta haɗu da iyalin ta bayan shekaru 8 da tayi a hannun yan ta’addan Boko Haram. Yan boko haram sun sace ta tare da tare da ƴaƴanta 4, ciki harda jaririyar shekara 4 a wani hari da suka kai a Bama a watan Satumbar shekara ta 2014.

Tun wannan lokacin ba a sake jin ɗuriyar su ba sai a lokacin da sojoji suka gudanar da wani atisaye a dajin Sambisa wanda ya kai ga ceto mutane da dama da yan ta’addan suka sace.

A lokacin da yan ta’addan suka sace su, sun kai su wani sansanin su da ake kira da Ukuba a dajin Sambisa, wanda anan ne aka raba Shetu da Ƴaƴanta 3 aka barta da karamar ƴar watanni 4, sannan suka ce da ita idan tayi yunƙurin guduwa zasu kashe ya’yan ta 3.

Tun wannan lokacin bata sake haduwa da Baba Shehu, Nana Fatima da kuma Tims Bamai Sangayama ba, suka bar ta da karamar mai suna Ashe yar wata 4.

Daga baya yan ta’addan suka aurar da ita ta dole ga wani dan ta’adda wanda ya riƙe ta yana bautar da ita tsawon shekaru 8.

Idan a za a tuna a watan Mayu, na bada rahoto cewa an ceto Shetu tare da wasu mata da yara da adadin su ya kai 900 a watan Mayun 2022 yayin wani atisayen sharar daji da sojojin 402 Special Forces Brigade su ka gudanar a dajin Sambisa wanda ya haɗa da runduna ta 134, 198, da kuma 199 Special Forces battalions ƙarƙashin Operation Haɗin kai wanda sune rukuni na 2 cikin masu Operation Desert Sanity.

Iyalan Shetu sun gane ta, bayan wani mai sharhi akan al’amuran tsaro Zagazola Makama ya wallafa labarin ceto su da akai a shafin sa na tuwita.

Bamai Sangayama wanda shine mijin Shetu ya bayyana godiyar sa ga Allah bisa share musu hawaye da yayi na shekara 8. Ya bayyana cewa yan ta’addan sun sace Shetu tare da ƴaƴanta 4 da suka hada da mata 3 da namiji ɗaya, saidai daya ce kaɗai ta bayyana daga cikin su, yayin da ragowar ukun suna can a rike a hannun Ƴan ta’addan.

Ya kuma bayyana cewa yanzu haka matar sa na asibitin kwararru na Umaru Shehu inda take samun kulawa daga wajen likitoci.

Labaran mata da suka tsinci kansu a cikin yanayi irin wannan na daga abubuwan da ba su cika bayyana ga al’umma ba da zasu kara bayyana irin cutarwar da Boko Haram/ISWAP sukai wa al’ummar yankin arewa maso gabas musamman a gabashin jihar Borno a tsawon shekarun da suka shude da yankin ya dinga fuskantar ta’addanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button