News

Ku dauki Dangana Kawai Tunda Kotu Ta Wancakalar Da Ku – Ganduje ga Abbas da sauran ‘yan APCn bangaren sa

Ku dauki Dangana Kawai Tunda Kotu Ta Wancakalar Da Ku – Ganduje ga Abbas da sauran ‘yan APCn bangaren sa

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya roki ‘yan APCn bangaren sa su dauki dangana.

Gwamnan Ya Kara Da Cewa tunda kotu ta wancalar da su kowa yayi biyayya Kawai.

A Wata ganawa da Gwamnan yayi da APCn bangaren sa karkashin shugabancin Abdullahi Abbas.

Ganduja ya ce zage-zage da kai ruwa rana ba zai sa a samu abinda akai Ga Gaciba ba.

”Kowa ya maida wukar a yi biyayya ga umarnin Kotu. Mu mutane ne masu da’a Kowa ya kwantar da hankalin sa.

Sai dai kuma Gwamnan bai fadi ko bangaren nasa za su daukaka kara ba.

Idan ba a manta ba sau biyu kotu na yin watsi da zaben APCn bangaren gwamna Ganduje ba. A cikin Nuwamba, kotu ta umarci su ganduje su baiwa bangaren Shekarau naira Miliyan 1 na bata masu lokaci da suka yi a kotu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu da ake zargin yan takifen bangaren Abdullahi Abbas ne suka cinna wa ginin APCn bangaren Shekarau wuta a Kano.

Sai dai ba ma yan jam’iyyar ba, yan gari wato mazauna unguwan suka fatattaki wadannan yan iska.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu daga cikin wadanda ake zargin sune suka aikata wannan abu.

Siyasar jihar Kano na ci gaba da kicimewa musamman jam’iyyar APC ganin yadda ta rabu gida biyu a jihar.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba domin an gano akwai wasu yan bangaren Ganduje dake sakawa a boye suna yin rajista da APCn bangaren Shekarau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button