Politics

Kusa Ido Kuga Yadda Zan Yiwa Kwankwaso Da Shekarau Ritayar Siyasa A 2023 — Inji A A Zaura

Zan yiwa Kwankwaso da Shekarau ritayar siyasa a 2023 — A A Zaura Kusa Ido Kuga Yadda Zan Yiwa Kwankwaso Da Shekarau Ritayar Siyasa A 2023 — Inji A A Zaura

Wanda jam’iyyar APC ta tsayar takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya gabanin zaben 2023, Abdussalam Abdulkarim (AA Zaura).

Ya lashi takobin cewa, zai kayar da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a yanzu, kuma dan takara a jam’iyyar NNPP, Malam Ibrahim Shekarau, a babban zaben shekarar 2023, tare da yi masa ritaya daga siyasa, dashi da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

AA Zaura ya bayyana haka ne a karshen satin da ya gabata, yayin ganawar sa da manema labarai a ofishin kamfen dinsa, inda yace haduwar Kwankwaso da Shekarau waje guda bata bashi tsoro.

Kuma lokaci yayi da su biyun zasu koma gefe, subar matasa masu tasowa a siyasa, kamar yadda Primetime News ta rawaito.

A cikin kalamansa, AA Zaura yace dukkan wadancan tsofaffin gwamnoni iyayensa ne, saboda haka yana matukar girmama su, amma dai yafi kyautuwa su matsa gefe suje su huta.

Ya kuma yi kira ga sauran abokan karawarsa na jam’iyyar APC da su hada hannu dashi domin kaiwa gaci, tunda dai shi Allah ya bawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button