News

Manyan Dalilin Da Yasa Amurka Tace A Goge Tiktok Daga Doron Duniya Batare Da Bata Lokaci Ba

Manyan Dalilin Da Yasa Amurka Tace A Goge Tiktok Daga Doron Duniya Batare Da Bata Lokaci Ba

Amurka ta umarci Goggle da su cire manhaja na Tiktok a manhajarsu

Daga: Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Kamar yadda muka sani kamfanin Tiktok na kasar China ne, wanda kowa yasan yadda Tiktok yayi barazanar kashe kasuwar Instagram da Facebook da suka kasance mallakin shahararren matashin me kudinnan an kasar Amurka wato Mark Zuckerberg, kowa dai yasan yadda alakar kasar China da Amurka yake na rashin jituwa da juna.

Umurnin dai ya biyo bayan zarge-zargen da kamfanin na Instagram ya shigar cewa Tiktok ya masa satar fasaha, zargin da kamfanin na Tiktok yace karyace kawai tsagoranta da hassada irin ta Instagram.

Amma su basu musu satar fasahaba, su Instagram dinne ma suka sace musu sabbin fasaharsu da su kadai sukazo da wannan fasaha, a yanzu haka dai ana dambaruwa, kwanaki hudu kacal suka ragewa Tiktok a manhajar Play store ko zasu sasanta ko ya zata kaya?

Idan har Play Store suka cire Tiktok, to Tiktok na kowa zaiyi Expire hakan zai hana kowa yin amfani da shi har sai kamfanin ya canza manhaja, Google Play Store ma dai mallakin Kasar Amurka ne.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button