News

Ministan Tsaro da Hafsoshin tsaro duk sun dunguma a Maiduguri a yau

Daga: Comr abdul m adam

Ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Magashi da Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Lucky Irabor gami da Shugabannin Ma’aikata duk sun dunguma zuwa birnin Maiduguri na Jihar Borno a yau Lahadi.

Ministan tare da Shugabannin tsaron sun hallara sansanin Sojin saman Najeriya dake birnin ne da misalin karfe sha ɗaya na safiyar yau din inda juma daga nan ne suka dunguma zuwa cibiyar rundunar yaƙi ta Operation Lafiya Dole don wata ganawar sirri da Kwamandar rundunar Janar Faruk Yahaya da kuma sauran manyan kwamandojin Yaki.

Manyan Hafsoshin tsaron sun hada da Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da Hafsan Sojin Sama Air Marshal Isiaka Alao gami da hafsan sojin ruwa Admiral Auwal Gambo wanda aka wakilce shi.

Ana sa ran Ministan tsaron zai zanta da manema labarai gabanni dunguma zuwa gidan Gwamnatin jihar Borno don ganawa da Gwaman Babagana Umara Zulum.

Wannan ziyara dai ba ta rasa nasaba da harin Ta’addanci da Kungiyar Boko Harama ta kai garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar inda suka hallaka mutane sama da sha takwas tare da jikkata wasu ashirin da daya, baya ga ɗaiɗaita Kayyakin gwamnatin Jihar da ma na Majalisar Dinkin Duniya.

Kazalika rahotanni sun bayyana cewa Ƙungiyar ta Boko Haram ta farmaki sansanin soji dake Jihar Yobe a Jiya Asabar lamarin da ya sanya ala tilas rundunar ta sanya dokar hana zirga-zirga a hanyar Damaturu zuwa Damboa zuwa Biu inda nan ne sansanin yake.

An ruwaito cewa Boko Haram din ta yi amfani ne da damar ta bayan da runduna ta musamman ta dake yaƙi a yanki ta fita wani aiki na musamman a wasu kauyuka dake kewaye da yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button