Politics

Bamu Dakatar Da Kwankwaso Ba- Uwar Jam’iyyar PDP

Uwar Jamiyyar PDP ta kasa tayi fatali da labarin da ake yadawa cewa wai ta kori Tsohon sanatan kano Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso Da Magoya Bayansa daga jam’iyyar ta PDP.

Kamar yadda sakataren yada labaran jam’iyyar ta kasa wato Kola Ologbondiyan Ya Sanar a yammacin lahadi Cewa.

Jam’iyyar PDP bata dakatar da Engr Rabi’u Musa Kwankwaso Ba Kuma Labarin da ake yadawa labarin kanzon kurege ne kawai bakomai ba.

Hakazalika jam’iyyar ta PDP ta kara jaddada Cewa kundim tsarin mulkin jam’iyar ya tanadi matakan da akebi domin dakatar da mamba a kwamitin zartarwa na kasa bawai kawai kara zube ake dakatar da mutumba.

Ologbondiyan ya kuma kalubalanci masu yada wannan labarin ka cewar su kawo matakan da sukabi domin zartar da wannan mataki.

Jam’iyyar ta kara da gargadin masu yada jita jita irin wanna da cewar sam bazata lamunci hakan ba domin hakan ka iya taba kima dakuma mitumcin jam’iyyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button