News

Muma Zamu Daina Yiwa Maza Kayan Daki Tunda An Kayyade Lefe-inji Kungiyar Mata

Mata: ‘Mun daina yi wa maza kayan daki tun da aka kayyade lefe’

Kungiyar ‘yan mata da zawarawa ta karamar hukumar Mayo Belwa a jihar Adamawa, ta gindaya sharudda ga duk maza dake son aure daga karamar hukumar.

Bbc Hausa Ta Rawaito Cewa Wadannan sabbin sharuddan na zuwa ne bayan da majalisar dake kula da harkokin addinin musulunci a karamar hukumar ta kayyade kayan lefe da maza za suyi yayin aure.

Shugabar kungiyar a karamar hukumar Fatima Ahmad, ta shaida wa BBC cewa sun kira taro a karshen makon daya wuce domin jin ra’ayin mata kan hukuncin na kungiyar harkokin addinin musulunci.

Fatima, ta ce “An sosa mana inda ya ke kaikayi ne, mun amince da dokar da kungiyar musulunci ta kafa, sai dai kuma mu ma korafinmu shi ne suna da tabbacin idan aka yi auren cikin sauki za a rike matan da ake aura? A yanzu hakan ana fama da yawan mace-macen aure, sai kaga an yi aure da sati daya ko wata daya ko shekara daya an saki mace ba tare da dalili mai karfi ba”.

Shugabar kungiyar, ta ce sun cimma abubuwa da dama a taron da suka yi in da ta ce “Abu na farko da muka cimma shi ne mutane susan cewa ba gwanjon mata akeyi a Mayo Belwa ba”.

Ta ce, ” Mun fitar da batutuwa game da da sadaki, zamu iya daga sadaki idan namiji zai biya sadaki da sauki to zai yi wa mace kayan aure, bayan haka kuma daga randa akayi aure ta koma gidanshi kayan sun zama nata”.

Fatima ta ce “Abu na biyu baza akai mace da komai daki ba ko da kuwa kayan kicin ne saboda muma bama bukatar komai daga wajen mazajen”.

Shugabar kungiyar matan ta kara da cewa ” Idan kuma har ba zasu iya yin kayan daki ba zasu ba wa mata kudi idan bazawarace daga dubu 300 zuwa sama sannan idan budurwace daga dubu 700 zuwa sama, kayan aure mun hakura da shi domin dama wani abune da ke ba wa mata wahala”.

“Abu na gaba kuma shi ne idan har namiji yazo ya tambayi auren mace to a ayi bincike game da lafiyarsa da kuma asalinsa, wadannan sune abubuwan da muke bukata majalisar harkokin addinin musulunci ta Mayo Belwa ta sanya hannu kansu” inji Fatima.

Fatima Ahmad, a wajen taron na su har da jami’an majalisar harkokin addinin musuluncin sun zo, kuma sun ji abubuwan da aka tattauna a wajen.

Shugabar kungiyar ta ce, tasowar wannan batun ne ya sa suka kafa kungiyar ‘yan mata da zawarawan kuma sun samu goyon baya sosai daga wuajen ‘yan matan gari da zawarawan har ma da majalisar dake kula da harkokin addinin musuluncin kanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button