Gwamnatin Jahar Gombe ta sanar da mutuwar mutum goma sha biyar 15 a yayin wani rikici da ya barke a yankunan Nyuwar da Jessu da kuma Yolde cikin karamar hukumar Balanga Wadda Ke makwabtaka da jahar Adawama.

Gwamnan jahar alhaji muhammadu inuwa yahaya ya ziyarci yankin yakuma bayyana cewa yanzu al’amura sun lafa sannan an sanya jami’an tsaro a guraren da aka sanya dokar hana fita.

Sannan gwamnan muhammadu inuwa yahaya ya kara da cewa tabbas anyi kone kone an kuma tafka mummunan asara ta rayuka dakuma dukiya.

Anan muke rokon ubangiji Allah ya zaunar da yankin mu na Arewa lafiya dama kasa baki daya

Click Here To Drop Your Comment