TALLAFIN AZUMI:
Pastor Yohana buru ya raba Tallafin kayan Abinci ga Musulmai mabukata a kaduna.

Daga Comr Abdul M Adam

Babban faston nan na jihar kaduna pst yohana buru ya raba tallafin kayan abinci ga musulmai domin watan ramadan a jihar kaduna.

A lokacin da yake raba kayayyakin babban faston yayi kira ga yan uwa musulmai akan zaman lafiya da kuma addu’ar zaman lafiya ga kasa da jihar kaduna.

Dama pastor yohana buru sananne ne wajen fafutukar ganin ansamu hadin kai tsakanin kiristoci da musulmai, sannan yana iya kokari wajen tallafawa musulmai musamman marassa karfi.

Click Here To Drop Your Comment