News

Ruwan Nono na Jarirai ne dan haka Ku daina Baiwa Mazajen ku’, Kwamishina ta Shawarci Iyaye mata

Ruwan Nono na Jarirai ne dan haka Ku daina Baiwa Mazajen ku’, Kwamishina ta Shawarci Iyaye mata.

Kwamishiniyar al’amuran jinsi A jahar Enugu, Hon. Peace Nnaji tana son mata su daina “baiwa mazajensu” tare da ajiye ruwan nonon ga jariransu.

Kwamishiniyar ta yi bayanin hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai da UNICEF ta shirya.

Ta yi bayanin cewa ba dai-dai bane maza su dinga shan maman matayensu inda ta ce an yi ruwan nono domin jarirai ba mazaje ba.

“Ruwan nono na jarirai ne ba na iyaye maza ba. Yakamata iyaye mata su dena shayar da mazajensu da ruwan mama na jariransu ne.

” Ba dai-dai bane iyaye mata su dinga kaucewa shayar da jariransu saboda tsoron kar mamansu ya zube”.

Kwamishinan ta kuma shawarci iyaye mata da su dinga shayar da jariransu har zuwa watanni 6 domin inganta lafiyarsu.

Prime news

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button