News

Sabon Bidiyon Da Masu Garkuwa Da Mutanen Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Suka Saki A Yammacin Yau Lahadi.

Sabon Bidiyon Da Masu Garkuwa Da Mutanen Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Suka Saki A Yammacin Yau Lahadi.

Kamar Yadda Zaku Gani Acikin Bidiyon, An Hango Mutane A Zube A Kasa Yayinda Wasu Ke Jawabi Game Da Halin Da Suke Ciki.

A Baya Kuma Gungun Masu Garkuwan ne Rike Da Makamai, Yayinda A Gaba Kuma Wani Ke Nadar Bidiyon Jawabin Da Mutanen Da Aka Kama Din Keyi.

Sun Bukaci Da Mutanen Suyi Magana, Ko Kuma Kira Ga Gwamnati Da Tazo Ta Biya Kudi A Sake Su. Ko Kuma Su Hallaka Su A Cewar Su.

Wannan Lamari Na Masu Garkuwa Da Mutane Dan Neman Kudin Fansa, Ya Zama Ruwan Dare Musamman Ma A Yankin Arewacin Nigeria.

Yayinda Mutane Ki Ganin Gwamnati Ta Gaza Cika Alkawuran Da Ta Dauka Na Samar Da Tsaro A Yankunan.

Inda Ake Ganin Masu Garkuwan Na Cin Karen Su Babu Babbaka A Duk Sanda Suka Ga Dama.

Wannan wani Faifan Bidiyo ne da ya fita na Mutane da Harin Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya rutsa dasu.

Muna Adduar Allah ya basu mahita ya basu kariya da kariyar shi.

Allah kuma yaba Jami’an tsaro fasahar yin nazarin wannan maboyar tasu yabasu ikon mamaye su Amin.

Wani abin lura da tunani kawo yanzu Bidiyo guda biyu kenan yana fitowa daga wurin waɗannan Mutanen suna batun cewa sunada Buƙatu wajen Gwamnati to wace Irin Buƙatar ce ?

Gadai Bidiyon Nan Ku Kalla

https://youtu.be/M5plkt0gsPY

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button