News

Shugaban Kasar Nijar Bazoum Mohamed Ya Baiwa Gwamnan Jahar Borno Lambar Yabo Yau A Jahar Damagaram

Shugaban Kasar Nijar Bazoum Mohamed Ya Baiwa Gwamnan Jahar Borno Lambar Yabo Yau A Jahar Damagaram

A Yau ne shugaban kasa Shugaban Jamhuriya Bazoum Mohamed ya bawa gwamnan Jahar Borno.

Babagana Zulum lambar yabo da ta daraja ta daya a NIGER wato “ORDRE NATIONAL DU NIGER” matsayin Grand Officier, a yau da safe a jihar Damagaram.

Tabbas Wannan Kyauta Ta Lambar Yabo Da Mai Girma Shugaba Bazoum Mohamed Zai Bawa Gwamnan Jihar Bornon

Abun Farin Ciki Ne Musamman Ma Gare Mu Yan Nigeria, Domin Sanin Kowa ne Cewa Ba Karamin Kokarin Gwamnan keyi ba Na Ganin An Kawo Karshen Masu Tada Kayar Baya.

Wanda Sune Ke Haurawa Jamhuriyar Nijar Din Suke Kaiwa Al’umma Hari Wadanda Basuji Ba Kuma Basu Gani Ba.

Anan Muke Addu’ar Ubangiji Allah Ya Taimaki Shugabannin Mu, Yakuma Hada Kawunan Su Ya Zaunar Da Kasashen Mu Lafiya, Ya Hada Kawunan Mu Amin Summa Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button