News

Shugabanni 4 Na Yan Bindiga Sun Mika Wuya A Jahar Katsina.

Shugabanni 4 Na Yan Bindiga Sun Mika Wuya A Jahar Katsina.

Daga Comr Abdul M Adam

Bincike da Arewa news eye sukayi sungano cewa maharan da suka mika wuya a jahar katsina sun kuma dawo da shanu 45 da suka sata tare da wasu muggayen makamai.

Arewa News eye tagano sunayen yan ta’adda dasuka mika wuya sun hada da Sale Turwa, Mani Turwa, Ado Sarki, da kuma Sani Mai-Daji bincike da akayi mungano cewa uku daga cikin su yan jahar katsina ne shugabannin ‘yan fashin guda hudu

a ranar Alhamis, 8 ga watan Afrilu sun mika wuya yayinda suka bayyana cewa sun daina aikata ta’addanci a jihar Katsina, biincike yanuna mana cewa sun mika wuya ne saboda wasu dalilan su da suka dade suna tunani akanta, daya daga cikin sun ya bayana cewa wasu mayan yan jahar suke sasu suke aikata wannan ta’addaci, wannan shine hanya da suke samun kudin a kai. Inji shi

Arewa news eye sun gano cewa maharan sun mika shanu 45 da kananan bindigogi biyu, da manyan bindigogin AK 47 24, da alburusai 109 na GMPG da sauran muggayen makamai, Mutane da dama suyi mamaki tayaya wannan yan ta’addan suke samun kayan aiki, bincike da arewa news eye ta gudanar yanuna cewa akwai masu safara musu wannan makaman a jahar, ana shigo musu da kayan ne a barauniyar hanya acikin jahar.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da ‘yan fashi, a cewar kwamandar nasu yace akwai yuwan nan bada jimawa ba wasu zasu mika wuya.

Mika wuyan su yana da nasabane ga samun sabani ga mutane da suke sasu wanann aiki, abincike da mukayi mungano akwai tarzoman tsakani yan ta’adda da kuma masu sasu su aiwatar da wannan aiki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button