Politics

Ganduje Ya Nemi Daliban Kano Su Zama Masu Biyayya

Ganduje Ya Nemi Daliban Kano Su Zama Masu Biyayya

Daga Comr Abdul M Adam

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nemi daliban jihar Kano da suke makarantu daban-daban a fadin kasar da ma kasashen waje da su kasance masu biyayya domin zama shugabanni da ‘yan kasa nagari.

Gwamnan ya nemi hakan ne a yayin da yake kaddamar da sabbin masu gudanarwa na babban kungiyar daliban jihar Kano na kasa, NAKSS a ranar Asabar a Kano.

A cewar gwamna Ganduje akwai bukatar sabbin shugabannin kungiyar su hada kawukansu domin ganin sun ciyar da kungiyar gaba da kuma samun tallafin gwamnati.

“a bangarenmu, zamu ci gaba da tallafa muku domin ku samu ku gudanar da ayyukan da suka shafi karatunku domin ku kammala cikin nasara. Na san kuna sane da shirinmu na karatu kyauta ga daliban firamare da Sakandare.

Ina mai shawartarku da ku hada kai da gwamnati domin ganin mun samu nasara a dukkanin shirye-shiryenmu. Mun bada damar karatu kyauta ne saboda ka da wadanda ba su da karfin tattalin arziki su ga cewa an nuna musu bambanci”, inji gwamnan.

“muna son ‘ya’yanmu su samu ilimi ko kai mai kudi ne ko talaka hakan ba zai hana iyaye tura ‘ya’yansu makaranta ba. Wannan yana da matukar muhimmanci a matsayinmu na shugabanni”, ya lurantar.

Gwamna Ganduje ya shawarci iyaye da ka da su ki tura ‘ya’yansu makaranta, inda ya ce idan suka yi hakan, idan yaran suka taso ba za su yafe wa iyayen ba.

Gwamna Ganduje har wala yau ya jinjinawa dukkanin daliban jihar dake makarantu daban-daban a kasarnan bisa irin kyakkyawan dabi’ar da suke nunawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button