![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/08/Screenshot_20220811-162324_1.jpg?resize=656%2C345&ssl=1)
Soyayya Ruwan Zuma: Wata Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Yin Wuff Da Wani Saurayin Da Suka Hadu A Tiktok
Wata kyakyawar budurwa baturiya ta kawo ziyara ga wani matashin Najeriya mai suna Mayor har gida A bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/08/FB_IMG_1660226156504.jpg?resize=300%2C169&ssl=1)
A bidiyon an ga budurwar tare da matashin da wasu abokansa suna shagali tare da ita zukekiyar baturiya A yayin da ya wallafa bidiyon a shafinsa na sada zumuntar TikTok.
Matashin ya bayyana farin cikinsa kan yadda baturiyar ta kawo masa ziyara har gida nigeria kuma ya godewa Allah Da Hakan.
A bidiyon da ya wallafa, an ga budurwar tana tafiya a kan wata siririyar gada tare da wasu abokan sa wadanda suke tare da matashin a koda yaushe.
Wani matashi ‘dan Najeriya ya wallafa bidiyo mai bada sha’awa daga yadda suka hadu da zukekiyar budurwarsa ta Amurka a TikTok.
Har a halin yanzu dai babu cikakken bayanin inda masoyan biyu suka hadu a zahiri. A wani bidiyo wanda ke nuna bayan haduwarsu ta farko, masoyan sun saka kaya iri daya yayin da suke ta shagali da shanawa a gaban teku.