News

Subhanillahi;! Bidiyon Yadda Da Da Uba Suka Mutu Yayin Yashe Rijiya A Jihar Kano.

Subhanillahi;! Bidiyon Yadda Da Da Uba Suka Mutu Yayin Yashe Rijiya A Jihar Kano.

Wani dattijo mai shekara 60, Malam Bala da dansa, Sunusi mai shekara 35, sun rasu a wata rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a Karamar Hukumar Wudil a Jihar Kano, a lokacin da suke aikin yasar rijiyar.

Wata sanarwa da kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba ta ce lamarin ya faru ne da safiyar Talata.

Ya ce: “Mun samu kiran gaggawa daga Ya
daga ce: ofishin kashe gobara na Wudil da misalin karfe 11:30 na safe daga wani lsmaila ldris, cewa wasu mutum biyu sun makale a cikin rijiya Nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru.

An kira wani mutum da dansa domin su
yashe wata rijiya, sun yi nasarar yashe ta, Amma, dan ya koma cikin rijiyar ya share ta a lokacin da ya makale ya kasa numfashi.

“Mahaifinsa ya bi shi don ceto shi, inda shi ma ya makale ya kasa numfashi saboda rashin iskar a cikin rijiyar’ cewar Abdullahi.

Ya ce duk da haka an fito da wadanda abin ya shafa daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu

Abdullahi ya ce an mika gawarwakinsu ga jamiin dan sanda na ofishin yan sanda model da ke garin Wudil, Felix Gowok

Da fatan Allah ya jikansu ya gafarta musu inda daga karshe muke da bukatar da ku danna alamar kararrawar sanarwa domin samun shirya shiryanmu a koda yaushe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button