Mijin Aljana Ummusabiyan Ya Karyata Kansa

Daga karshe dai Mijin Aljana UMMUSABIYAN ya karyata kansa da kansa, ya ce yana yin hakan ne don ya sami na shinkafa da masara.

Gwamnatin jihar Kano ce dai karkashin jagorancin mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin addinin Musilinci ta gayyaci Malamin wanda ya yi karyar ya auri Aljana domin yi masa tambayoyi, sai dai tun kafin a yi nisa ya karyata kansa sannan ya nemi afuwa ga Gwamnati da jama’ar Jihar Kano.

 

Ku Kalli Bidiyon Anan https://youtu.be/t3_psYQK3KU

Click Here To Drop Your Comment