News

Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Alkali A Jihar Enugu

Rahotanni Daga Jihar Enugu Na Cewa Wasu ‘yan bindiga Dadi sun Harbe tsohon alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter ya nuna yadda ‘yan bindigar suka zaro Mai Shari’a Stanley Nnaji daga motarsa sannan suka harbe shi a tsakiyar titi, yayin da sauran motoci ke tsaye a bayan tasa.

 

Lamarin dai na zuwa ne yayin da ake zaman ɗar-ɗar a yankin Na kudu maso gabas sakamakon umarnin da ƙungiyar Yan IPOB masu son kafa ƙasar Biafra Wanda ta bayar na zaman gida domin tunawa da ranar yaƙin Biafra.

A kwanan nan, ‘yan bindiga na kai hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda da na hukumar zaɓe ta INEC kuma hukumomi na zargin ‘yan IPOB ne ke kai su.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Enugu Mohammed Aliyu ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button