Shugaban Kungiyar izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Ya Umarci Duk Kan Malaman Kungiyar Izala Dake limancin masallacin juma’a Da Su Gudanar Da Addu’a Ta Musamnanman domin jana’izar Marigayi COAS, Laftanar Janar Attahiru Ibrahim da sauran jami’an da suka mutu.

Mallam Ya Wallafa Kamar Haka A Shafinsa na Sada Zumunta.

Inda Ya Rubuta Cewa.Na umarci dukkan Limaman da ke jagorantar Sallar Juma’a a dukkan Masallatan JIBWIS na kasar nan da su gabatar da Addu’oi na Musamman na Kasa domin jana’izar Marigayi # COAS, Laftanar Janar Attahiru Ibrahim da sauran jami’an da suka mutu. Irin wannan Addu’o’in yakamata ayi don samun nasara & lafiya na sabon # COAS, Manjo Janar Farouk Yahaya.

Click Here To Drop Your Comment