News

Tirqashi: Aisha Buhari Nashan Suka Kan kalaman datayi Akan Fita Turai Neman LaFiya

Aisha Buhari ta bayyana haka ne lokacin da bi sahun shugaba Muhammadu Buhari da sauran muƙarabban gwamnati wajen kaddamar da asibitin da ke cikin fadar shugaban ƙasa a Abuja a ranar Juma’a.

Mai ɗakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce a ganinta babu buƙatar shugabannin Najeriya su fita waje don neman lafiya bayan kaddamar da kaddamar da asibitin fadar shugaban ƙasa wanda ya laƙume kuɗi naira biliyan 21.

Matar shugaban ƙasar Najeriyar ta faɗa wa manema labarai cewa ta bijiro da batun ganin an samar da asibitin ne shekara shida da suka gabata, bayan ɗaukar tsawon lokaci da mijinta ya yi a waje domin neman lafiya.

Ta tabbatar da cewa ganin an samar da asibitin a yanzu, shugabannin ƙasar da iyalansu ba sa buƙatar fita waje neman lafiya, sai dai su kawo ƙwararrun likitoci domin taimaka wa takwarorinsu na ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button