News

Wata Kotun Shari’a A Zamfara Ta Raba Aure Saboda Girman Mazakutar Mijin

Wata Kotun Shari’a mai zamanta a jahar zamfara ta raba wani ma’aurata Saboda girman mazakutar mijin.

Wani rahoto da muka samu daga shafin jaridar legithausa ya bayyana cewa wata ta roki Alkali da ya raba aurenta da mijinta saboda girman mazakutar sa.

Matar ta bukaci a raba auren nasu sati daya tak da yin auren. Bayan ya kusance ta sau 2 Anan ta gane bazata iya jurewa girman mazakutarsa ba.

Shima Anasa bangaren Mijin Matar ya aminta da kotun data raba auren nasu tunda taga bazata iya dashi ba.

Wannan lamari dai ya faru ne a kotun shari’a dake samaru a gusau din jahar zamfara

Haka zalika jaridar the nation ta rawaito cewa matar mai suna aishatu dannupuwa mai yaya uku ta auri mijin nata na biyun ne bayan mijinta na farko ya mutu.

A jawabin aisha dannupuwa ta bayyanawa kotu cewa a al’adarsu ana fara tarewa ne a gidan iyaye daga bisani sai a koma a tare a gidam miji bayan daura auren.

Dayazo ya kusance ni a maimakon nasamu nutsuwa sai akasin haka ta faru saboda tsabar girman mazakutar tasa.

Aishatu dannupuwa taci gaba da shaidawa kotu cewa tun daga wannan lokacin ne ta samu ciwo a gabanta sai ta fara shan maganin gargajiya wanda mahaifiyarta ta bata. Sannan ta kara da shaida mata cewar sannu a hankali watarana zata saba.

Bayan kwanaki biyu sai ya sake kawomin ziyara tare da sake kusantata daga nan ne nagane sam bazan iya zama dashi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button