Rahotanni Daga Jaridar TVC na cewa, Majalisar Wakilan Nigeria Tayi Watsi da wani kudiri da ya bukaci da a sallami tare da bincikar ministan sadarwa Dr. Isa ali pantami Kamar Yadda Wani dan majalisa ya bukata.

Tun a farkon wannan watanne cece kuce ya barke kan batun wani murya da aka jiyo ministan nayi addu’a ga wasu mutane.

Lamarin da ya haifar da cece kuce a shafukan sada zumunta dama kasa baki daya.

A yayinda shehin malamin kuma minista ya fito ya bayyana cewa wannan batu da akaji acikin murya na nuna goyan baya ga wasu mutane dake ikirarin jahadi yayi sune a wasu shekaru da yawa da suka shude.

Inda ya bayyana lamarin a matsayin kuriciya.

Lamarin da yasa wasu mutane musamman daga kudancin kasar tura bukatar tsige ministan ga majalisar wakilan kasar

Click Here To Drop Your Comment