News

Yanzu-Yanzu Yan Bindiga Sun Sake Sace Wasu Daliban Jami’a A Jahar Kaduna

Rahotanni Daga Jahar Kaduna Na Cewa Wasu Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba Da Wasu Daliban Jami’ar Green Field Dake Jahar Kaduna.

Yan bindigar sun farma makarantar ne a daren talata kamar yadda jaridar thecable ta rawaito.

Dafari yan bindigar sun bude wuta domin tsoratar da mazauna yankin kafin daga bisani su dura makarantar tare da awon gaba da daliban.

Jami’ar green field jam’ace mai zaman kanta wadda ke hanyar kaduma zuwa abuka a karamar hukumar chikum, daya daga cikin guraren da yan bindiga suke.

Ya zuwa yanzu ba’a samu jin ta bakin kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida na jahar kaduna samuel Aruwan ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button