Jami’ar Maryam Abacha ta karrama Marigayiya Haneefa…

Biyo bayan zargin garkuwa da kisan yarinya Haneefa da wani malaminta na makarantar boko mai suna, Abdulmalik Muhammad Tanko, yayi.

A baya bayan nan, a yankin Kwanar Dakata dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Reshen jami’ar Maryam Abacha dake Nigeria, ta karrama Marigayiya Haneefa ta hanyar sanya sunanta a guda cikin titinan makarantar.

Yayin tattaunawarsa da manema labarai, shugaban jami’ar Farfesa Adamu Gwarzo, ya bayyana rasuwar Haneefa a matsayin mutuwa mai taba zuciya.

Wanda kuma hakan ne yasa suka ga dacewar su sanya sunanta a makarantarsu, domin tunawa da ita.

Mahaifin Haneefa, Abubakar Abdussalam, shi ne ya yanka kyallen bude allon da aka rubuta sunan Haneefa a guda cikin titinan jami’ar, ya bayyana godiyarsa bisa wannan karamci da sadaukarwa da aka nuna masa.

📷 Facebook/President MAAUN

Nasara Radio 98.5 FM
31/1/2022

Click Here To Drop Your Comment