News

Yadda Akai Jana’izar Tokar Gawarwakin Bayin Allah 42 Da ƴan Bindiga Su ka ƙona Su Da Ran Su A Sokoto.

Yadda Akai Jana’izar Tokar Gawarwakin Bayin Allah 42 Da ƴan Bindiga Su ka ƙona Su Da Ran Su A Sokoto

Daga Muhammad Aminu Kabir

“INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJI’UUN!

An yi jana’izar tokar gawarwakin mutane 42 da ƴan bindiga suka kashe tare da ƙona su da ran su a jihar Sokoto.

Yadda aka gudanar da jana’izar tokar gawarwakin bayin Allah 42 ciki har da mata da ƙananan yara da ƴan bindiga su ka kashe tare da ƙona su da ran su a akan hanyar Sabon Birni zuwa Isah, waɗanda zasu tafi Abuja domin neman abincin da za su ci.

Wannan tashin hankali da mi yayi kama ace ƴan Ta’adar nan yanzu sun daina ma satar Mutane sai dai kisan Gillah irin wannan Hasbunallahu wa Ni’imal wakil, lallai ya kamata Al-umma ta tashi ta kare kanta ta duk hanyar da zata Iya.

Ayi ƙoƙarin taƙaita zirga zirga a wuraren da aka san suna da hatsari Musamman ma dai yankin Isa da sabon Birni na jihar Sokoto har sai an samu sauƙin wannan Ta’adancin.”

Muhammad Aminu Kabir

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button