News

Yanzu Yanzu Bidiyon Yadda Aka Kusan Kashe Wanda Yayi Batanci Ga Annabi a America An Daba Masa Wuka a Wuya

Yanzu Yanzu Bidiyon Yadda Aka Kusan Kashe Wanda Yayi Batanci Ga Annabi a America An Daba Masa Wuka a Wuya

Marubucin, wanda aka shafe tsawon shekaru ana masa bazaranar kisa saboda ya rubuta wani littafi, ‘The Satanic Verses,’ da ake zargin ya yi batanci ga Annabi SAW, an farmake shi ne a New York.

A wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa, ta ce wani mutumi ya yi fitar burgu zuwa kan dandamalin da Marubucin ke shirin gudanar da Lakca, inda ya rinka bugunsa yana daɓa masa wuka.

Shaidun da lamarin ya auku a gaban su, sun ce mutumin ya farmaki Mista Rushdie ne yayin da ake gabatar da shi a gaban taron Jama’a.

Bayanai sun nuna cewa mahalarta taron ne suka yi kokarin zuwa kan Dandamalin domin kai masa ɗauki, amma ana tsammanin an daɓa masa wuƙa a wuya.

A halin yanzu, ba’a san halin da Fitaccen marubucin ke ciki ba, amma ‘yan sanda sun tabbatar da cewa an daɓa wa wani mutumi wuƙa, ba su fayyace ko waye ba a bayanan su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button