Religion

MUSULMCI DADI: Akaron Farko Jaruma Akuapem Poloo kiristan data musulinta tayi magana game da sauya shekarta zuwa Musulinci

MUSULMCI DADI: Akaron Farko Jaruma Akuapem Poloo kiristan data musulinta tayi magana game da sauya shekarta zuwa Musulinci

Yar wasan Ghana kuma mai wayar da kan jama’a “Rosemond Brown” wacce aka fi sanida Akuapem Poloo, ta fito ta bayyan dalilin ta na sauya sheka daga addinin Kirista zuwa Musulunci.

Jarumar kwanan nan ta sanar da sauya shekar ta zuwa addinin musulunci kuma hakan ya jawo cece-kuce tsakanin jama’a, Poloo ta wallafa bidiyo a shafinta na instagram tana bayyana dalilin da yasa ta sauya shekar.

Ta bayyana jin dadin ta na zama musulma sannan ta roki ‘yan Ghana dasu mutunta ra’ayin ta, jarumar dai ta dau damarar killace jikin ta, tare da daukar alkawarin daina bayyana tsiraicin ta.

Sai dai zata cigaba da rike sunan dandalin tana yanar gizo tunda tace tayi magana da malamin ta kan cewar, sunan dandalinta bai saba wa duk wata ka’ida ta Musulunci ba sabida haka zata cigaba da amfani da shi.

A karon farko da akayi comment akan postdin ta, kada ki bari kowa ya baki shawara yadda zaki sa kaya, abin da nake rokonki shine sallolinki guda 5 ki rike, Allah yana kallon zuciyar ki rashkele2000 ya rubuta.

Kai gaskia kinyi kyau cikin mayafi Allah ya kara albarka yamiki jagora Mizto by yayi sharhi: kowane addini kika koma ina tare da ke, dole mutum ya soki da duk abin da kuke yi ko zaba💓💓.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button