News

Yanzu-yanzu Kotu Ta Tasa Keyar Mu’az Magaji Dan Sarauniya Gidan Gyaran Hali

Kotu Ta Aike Da Mu’az Magaji Gidan Gyaran Hali

Aliyu Samba

A Ranar litinin ne kotun Majistrate dake zaman ta a Nomansland ta cigaba da sauraren karar da gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya shigar da Engr Muaz Magaji wanda aka fi sani da ɗan sarauniya.

Ana zargin wanda ake ƙara da aikata laifin kalaman ɓatanci, bata suna, kalaman tunzuri da kuma yada karya a hakkin gwamnan jihar Kano.

Mai Shari’a Aminu Gabari ya fara zaman shari’ar na yau da misalin karfe 12:45 na rana, yayin da Barrister Garzali Ahmad Sulaiman, Barrister Aisha Abdurrahman Usman da kuma Barrister Abdurrazak A Ahmad suka bayyana a kotu a matsayin lawyoyin wanda ake ƙara.

Gabanin fara gabatar da shari’ar, an karantawa wanda ake ƙara laifukan da ake zarginsa da sa, wanda suka haɗa da laifin ɓata suna, kalaman zagi da gangan, kalaman tunzuri da kuma kazafi. Saidai wanda ake ƙarar ya musanta zargin duk da cewa yayi korafin samun matsalar ji a kunnen sa, ya tabbatar wa kotu cewa yaji tuhumar kuma ya musanta.

Masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Barista Wada .A Wada ya nemi kotu da ta sanya wata rana domin cigaba da gabatar da Shari’a, saidai lawyoyin wanda ake ƙara sun bukaci a basu belin wanda ake ƙara, dogaro da cewa yana cikin mawuyacin hali na rashin wadatacciyar lafiya, kuma babban mutum ne da bazai ketare beli ba saboda tuhumar da ake masa a gaban kotu.

A nasu ɓangaren, lawyoyin da ke gabatar da kara sunyi suka akan bukatar beli, inda suka bayyana cewa babu wata hujja daga likita da ta bayyana cewa wanda ake ƙara din bashi da lafiya kamar yadda doka ta tanada, sannan kuma laifin nashi yayi ne da gangan musamman a yanzu da mutane ke amfani da kafar sada zumunta dan batanci ga manya.

Sannan ya kara da cewa gudun kada wanda ake ƙara ya kawo katsalandan akan shari’ar da shedun da za a gabatar wa kotu, ya bukaci kotu tayi watsi da batun beli.

Saidai lawyan wanda ake ƙara yayi suka inda ya bayyana cewa, wannan kotun itace ta bada umarnin a kai wanda ake ƙara asibitin shedikwatar ƴan sanda dake Bompai a zaman da ya gabata, wannan ya isa sheda cewa dukkan ɓangarori uku sun tabbatar da cewa wanda ake ƙara na bukatar ganin kwararren likita.

A ƙarshe mai Shari’a Aminu Gabari ya bayyana cewa, a kai wanda ake ƙara zuwa gidan gyaran hali, sannan kuma a bashi kulawa a asibitin gidan gyaran hali. Ya kuma ɗage shari’ar zuwa 3/2/2021.

©Jarida Radio
31/1/2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button